Najeriya

Hukumar ‘Yan sandan Najeriya ta amsa janyewa Kakakin Majalisa Aminu Waziri jami’an tsaro

starconnectmedia.com

Sakamakon sauya shekar da Kakakin Majalisar wakilan Najeriya Aminu Waziri Tambawal ya yi a bayyane, zuwa Jam’iyyar APC mai adawa a kasar, Rahotanni na nuna cewar an janye daukacin jami’an tsaron da ke gadin sa a Gidansa da kuma Ofis

Talla

Rundunar ‘yan sandan Nigeria ta ce ita ce ta bayar da umarnin janye jamai’an tsaron da ke kula da kakakin majalisar wakilan kasar Aminu Waziri Tambuwal.

Sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce Mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sandan, Suleiman Abba ne ya bayar da umarnin hakan, kamar yadda a cewar rundunar ‘yan sandan ta ce ke kumshe a kundin tsarin julkin kasar, na shekarar 1999 ya tsara.

Sai dai masana harkokin shara’a a kasar sun fara kushewa matakin da rundunar ‘yan sandan kasar ta dauka, ga mutumin da ke kan muhimmin matsayi a Najeriyar.

Barrister Solomn Dallung yace matakin wani karan tsaye ne ga tsarin mulkin kasar.

Ficewar da Kakakin Majalisar Aminu Waziri Tambawal ya yi daga PDP dai na zaman babban kalu-bale ga Jam'iyyar wadda a baya, kuri'un yankin da Kakakin Majalisar ya fito wato Arewa maso yamma, na daga cikin muhimman ababen da suka taimakawa shugaba Jonathan mai mulkin kasar samun nasara a zaben da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.