Ilimi Hasken Rayuwa

Matsalolin ka'idojin rubutun Hausa

Wallafawa ranar:

Shirin  Ilimi Hasken rayuwa ya yi nazari ne game da ka’idojin rubutun Hausa tare da  Mashahurin Malamin Hausa, Farfesa Abdulkadir Dangambo.

Farfesa Abdulkadir Dangambo na Jami'ar Bayero a Kano
Farfesa Abdulkadir Dangambo na Jami'ar Bayero a Kano Freedom radio kano
Talla

Idan masu saurare ba su manta ba a makon daya gabata mun yi bayani game da taron duniya na nazarin hausa da aka gudanar a Jami’ar Bayero inda muka tattauna tsarin  ilmantar da hausa a cikin harshen hausa, musamman ta fuskar  kimiya da safaha.

A wannan Makon shirin ya diba matsalar ka’idar rubutun Hausa.
Ko wane harshe a duniya yana da na shi ka’idojin rubutu, domin amfani da ka’idojin rubutun ne ke tayar da ma’ana tare da fahimtar abin da aka rubuta.

Ana cewa “Hausa gagara mai ita”, wannan kuma ya shafi matsalar aiki da ka’idojin rubutu ne.

Turawa da dama sun yi kokarin samar da ka’idojin rubutun Hausa tun a wajajen karni na 16 zamanin mulkin Turawa da karatun Boko ya samo sali. 

Kodayake an soma yin rubutun Hausa ne a cikin Ajami, amma zuwan Boko aka kara inganta hausa.

A wajajen karni na 18 turawa sun yi rubuce rubucen kalmomi na Hausa da dama tare da kokarin fito da tsarin rubutu haruffan da ake yi wa lankwasa.

To sai a zamanin nan rubutun hausa na fuskantar kalubale, ta bangaren bin tsarin ka’idojin rubutu tsakanin masu amfani da harshen.

Akan haka ne Farfesa Abdulkadir dangambo mashahuran malamin Hausa ya gabatar da takarda mai taken “Ka’idojin rubutu ina muka dosa” a taron duniya na nazarin Hausa da aka gudanar a Jami’ar Bayero.

Kuma shirin ya tattauna da shi, shin ko wadanne matsaloli ne Hausa ke fuskanta ta fuskar ka’idojin rubutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI