Nigeria

Wani babban jami'in gwamnatin jihar Kebbi yayi murabu a Nigeria

Taswirar Jihar Kebbi dake Nigeria
Taswirar Jihar Kebbi dake Nigeria

Rahotannin da dake fitowa daga jahar Kebbi a arewacin Nigeria, na nuna cewa shugaban ma'aikatan gidan gwannatin jihar, Alh Abdullahi Muhammed Lamba yayi murabus daga mukaminsa.
Wakilinmu a yankin yace cikin daren jiya ne shugaban ma'aikatan ya bayyana murabs din nasa, kan abinda ya kira rashin gamsuwa da yadda ake tafiyarda aiki a jahar.
Abdullahi Muhammed Lamba yace Tsawon lokacin da ya share a bisa mukamin ba wani aiki da aka bashi abinda ya bayyana da cewa jiran office kawai yake yi ba aiki ba.
Kawo yanzu dai gwannatin jahar bata maida martani kan murabus din ba.