Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Matsalolin Fassara a gidajen Rediyo

Sauti 10:10
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou, tare da Christophe Boisbouvier, na RFI a dakin watsa shirye shiryen Rediyo Faransa a Paris
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou, tare da Christophe Boisbouvier, na RFI a dakin watsa shirye shiryen Rediyo Faransa a Paris Paulina Zidi/RFI
Da: Awwal Ahmad Janyau

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya yi nazari ne game da Fassara musamman aron kalma daga wani harshe zuwa harshen Hausa sannan shirin ya tabo matsalolin fassara, a gidajen Rediyo.

Talla

Aikin Fassara na daga cikin hanyoyin da ke taimakawa harshe ya bunkasa, kuma babban abin da ake sa wa gaba a aikin fassara shi ne kokarin ganin am fahimtar da Hausawa akan wani sako da ke kunshe a wani harshe, kuma dole sai mai fassara ya lakanci harsunan guda biyu da al’adunsu kafin yin fassara mai ma’ana.

Akwai taron duniya da aka gudanar a Jami’ar Bayero akan nazarin hausa, kuma fassara na daga cikin ayyukan da mazanarta suka gabatar da takarda akai.

Shirin ya tattauna da Dr Aliyu Musa da Dr Yakubu Azare na sashen koyar da harsunan Najeriya a Jami’ar Bayero Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.