Najeriya

Hankulla sun fara kwantawa a Jos bayan tashin Boma-Bomai

nydailynews.com

Ya zuwa yanzu dai al’amurra sun fara lafawa, bayan tashin wasu Boma-Bomai da suka yi sanadin mutuwar akalla mutane 13 a birnin Jos na jihar Filato

Talla

Gwamnatin jihar dai na danganta wadannan hare-haren da cewar mai yuwa ne suna da alaka da kungiyar Boko Haram, lura da yadda ake ta danganta ire-iren wadannan hare-haren da ake kai wa a wasu jihohi ga kungiyar ta Boko Haram.

Mai magana da yawun fadar gwamnatin jihar Mr Pam Ayuba ya ce suna ganin cewar tashin Boma-Boman na matsayin manuniya kan yadda hare-haren Boko Haram ke dada watsuwa zuwa wasu yankuna.

Tashin Bomb din day a auku ne da musalin karfe 6 na yammacin ranar Alhamis, a wata Kasuwa da ke kusa da Tashar Motar Taminus, kuma babu nisa daga wurin da aka samu tashin wani Bom a cikin watan Mayun da ya gabata, day a yi sanadin mutuwar mutane 118.

Pam Ayuba ya ce daman gwamnatin jihar ta samu bayannan sirri da suka tabbatar masu cewar hakan za ta faru, amma a cewarsa harin baya da alaka da Siyasa.

Garin Jos da ke a yankin Arewa ta tsakiya inda Musulmi ke da yawa a yankin Arewaci, Kirista kuwa a yankin Kudanci, ta kasance gari mai matukar wuyar zama lura da yadda a baya ba’a ga-Maciji da juna tsakanin al’ummar Musulmi da Kiristocin kasar.

Daruruwan mutane ne suka mutu a lokacin da aka gabatar da sakamakon zaben shekarar 2011, amma inji Pam Ayuba, an kammala zaben fidda gwani na Jam’iyyun Siyasa a cikin jihar a Makon da ya gabata, ba tare da samun tashin hankali a sau daya ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.