Najeriya

Kotu ta yi Umurni a maida Jakolo a matsayin Sarkin Gwandu

dailypost.ng

A Najeriya wata Kotu a jihar Kebbi, ta bada umurnin a sake mai da tsohon Sarkin Gwandu Alhaji Almustafa Haruna Jakolo a kan Karagar mulkin masarautar ta Sarkin Gwandu

Talla

Idan ana iya tunawa, a shekarar 2005 ne gwamnati a wannan lokacin ta bada umurnin a fidda tsohon Sarkin daga Karagar jagorancin masarautar ta Gwandu, abin da ya baiwa Sarkin Gwandu na yanzu Alhaji Iliyasu Bashar damar dare Karagar mulkin kasar Kabi.

A hira da ya yi da Faruk Muhammad Yabo, Alhaji Almustapha Harun aJakolo ya bayana hukuncin Kotun a matsayin nasara da ya samu, sai dai ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankali kar a yi wani abu da bai dace da Doka ba.

Yace a nashi bangaren ba zai yiwu ya dauki matakin yin ramuwar gayya ga mutanen da suka samu takon-Saka da shi ba a baya, domin shi na kowa da kowa ne.

Bayan bayyana hukuncin Kotun, Rahotanni daga Birnin Kebbi na cewar an ga mutane na ta farin ciki da abinda ya faru na yanke hukuncin maida Jakolo a kan Kragar mulkin masarautar Sarkin Gwandu.

Sarautar Sarkin Gwandu wadda ke zaman ta farko a yankin kasar kabi, sarauta ce babba daga gidan Mai martaba Sarkin Musulmi na Sakkwato.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.