Jolly Phonics: Tsarin Koyarwa ta hanyar amfani da furucin sauti

Sauti 10:11
Darasin Jolly Phonics a Makarantar Firamare ta Tudun wada a garin Gusau Jihar Zamfara Najeriya.
Darasin Jolly Phonics a Makarantar Firamare ta Tudun wada a garin Gusau Jihar Zamfara Najeriya. RFI Hausa/Awwal

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya yi bayani ne game da wani sabon tsarin karatu da ake koyar da yara a makarantun Firamare wanda ya kunshi koyar da bakake ta hanyar amfani da furucin sauti don gina kalma wato tsarin da ake kira Jolly Phonic.

Talla

A kasar Birtaniya ne aka samar da tsarin Jolly Phonics domin karartar da yara yadda zasu yi karatu da rubutu ta hanyar amfani da furucin sauti.

Tsarin na Jolly Phonics ya kunshi harrufa 42, kuma akwai dubarun da ake bi domin koyar da yara cikin raha da wasa da waka.

Jihar Zamfara a Najeriya ta shigo da wannan tsarin a wasu makarantun Firamare domin koyar da yara yadda zasu lakanci rubutu da karatu da wuri ba tare wani wahala ba.

Shirin Ilimi ya kai ziyara Makarantar Firamare ta Tudun Wada Gusau daya daga cikin makarantun da ake koyar da wannan sabon tsarin na Jolly Phonics, kuma Shirin ya zanta da Hedimasta Musa Almu Gusau game da tsarin tare da kuma zantawa da daliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.