Bakonmu a Yau

Dadi Umaru Jami’in Red Cross

Sauti 04:09
Jami'an kungiyar agaji ta red cross suna raba gayan agaji a sansanin 'Yan gudun hijira a Dawaki
Jami'an kungiyar agaji ta red cross suna raba gayan agaji a sansanin 'Yan gudun hijira a Dawaki REUTERS/Stringer

Sakamakon tashe-tashen hankula da ake fama da su a jihohin Borno na Yobe da Adamawa, yanzu haka yawan mutanen da suka gudu daga yankin zuwa jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar sunkusa dubu dari. Wadannan mutane dai na samun kulawa ne daga kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa da kuma gwamnatin jamhuriyar Nijar. Mai magana da yawun kungiyar bayar da agaji ta Red Cross Dadi Umaru, ya yi bayanin irin tallafin da suke bayar a tattaunawar shi da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.