CAF

Yaya Toure ya zama Gwarzon Afrika karo na hudu

Yaya Toure na Cote d'Ivoire a lokacin da ya karbi kyautar gwarzon Afrika karo na hudu
Yaya Toure na Cote d'Ivoire a lokacin da ya karbi kyautar gwarzon Afrika karo na hudu REUTERS/Akintunde Akinleye

Dan wasan Manchester City Yaya Toure ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika karo na hudu a Jere bayan ya samu rinjayen kuri’u fiye da abokan takararsa Vincent Enyeama Golan Lille da Najeriya da kuma dan wasan Borussia Dortmund Pierre-Emerick na Gabon.

Talla

Golan Najeriya Vincent Enyeama ya taya Yaya Toure murnar a bayan kammala bikin da aka gudanar a birnin Lagos.

Yaya Toure ya kafa tarihi a Afrika a matsayin wanda ya lashe kyautar karo hudu a jere da jare. Kodayake Eto’o ya taba lashe kyautar sau hudu.

A shafin Vincent Enyeama na Istagram Golan ya taya Toure murna tare da godewa Ubangijinsa da magoya bayansa akan kwarin guiwar da suke ba shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.