Ilimi Hasken Rayuwa

Sabbin hanyoyin samun Makamashi

Sauti 10:11
Ana Samun Makamashi daga Hasken rana
Ana Samun Makamashi daga Hasken rana © NTF Energy

Sharhin shirin Ilimi-Hasken-Rayuwa na wannan makon, ya yi duba ne kan sabbin hanyoyin samun makamashi kamar yadda wasu kasshe na duniya ke amfani da su, da kuma yadda kasashe masu tasowa zasu iya cin gajiyar wadannan hanyoyin a saukake.

Talla

Daya daga cikin manyan kalubalen da kasashe masu tasowa ke fuskanta ta fannin tattalin arziki da ci gaba, shi ne na karancin makamashi. A galibin wadannan ana dogara ne kan makamashi daga madatsun ruwa ko Dam-Dam wajen samun wutar lantarki. Sai dai binciken masana a fannin kimiyya da fasaha na tabbatar da wasu hanyoyi samun makamashi a saukake.

Bisa fassara dai makamashi shi ne sinadarin da Dan Adam kan yi amfani da shi domin biyan bukatun sa na yau da kullum tun daga hasken wuta zuwa samun iskar Gas na girki.

Al'umma kan dogara ga makamashi domin inganta rayuwa da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Sai dai bisa tsadar nau'in makamashin wutar lantarki da galibin kasashe masu tasowa kan dogara akai, binciken masana a fannin kimiyya da fasaha na tabbatar da wasu hanyoyi samun makamashi a saukake.

 

Shirin ya tattauna da masana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.