Nigeria

Amnesty tace dakarun Najeriya na sane da harin da aka kai Baga da Munguno

Wasu dakarun sojan Najeriya
Wasu dakarun sojan Najeriya AFP PHOTO/ PIUS UTOMI EKPEI

kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty tace rundunar sojan Nigeria na sane da mummunan harin da kungiyar Boko haram ta kai a garuruwan Baga da Monguno, kafin ‘yan bindigar su dirar wa garuruwan na yankin arewa maso gabashin kasar. Cikin rahoton da ta fitar yau Laraba, kungiyar tace, duk da samun bayanai kan harin, amma rundunar sajan bata bayar da umarniun kai dauki a yankin ba.Akwai yuwuwar harin na ranar 3 ga wannan watan Junairu ya yi sanadiyyar rasa ran daruruwan mutane, ko ma fiye da haka, yayin da karbe barikin Monguno da ‘yan Boko Haram din suka yi, ke matsayin babban koma baya ga dakarun Nigeria.Kungiyar ta Amnesty tace ta sami bayani daga manyan hafsoshin soja, da ma wasu majiyoyin, dake cewa an sanar da jami’an tsaron kasar cewa ‘yan kungiyar ta Boko Haram na shirin kai hari a garuruwan 2, amma suka ki bayar da umarnin kai dauki.Kungiyar ta kuma kara da cewa ‘yan bindigan sun gargadi fararen hulan dake yankin, inda da dama suka tsere kafin lamarin ya faru.Radiyon Faransa ya nemi nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar sojan Nigeria Chris Olukolade, amma bai amsa waya ba.A baya, kungiyar ta Amnesty ta zargin sojan Nigeria da irin wannan sakacin, a lokacin da aka yi awon gaba da ‘yan matan Chibon, cikin watan Aprin bara, a jihar ta Borno.