Najeriya

Hukumar zaben Najeriya ta fito da Alkalumman masu Katin jefa kuri’a

Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega RFI/Bashir

A Najeriya hukumar zabe mai zaman kanta ta kasra ta fidda Alkalumman yawan mutanen da suka yi rajistar Katin zabe ta wuccin gadi, da kuma wadanda aka riga aka baiwa Katin ta dindindin na jihohi da kuma na kasa baki daya

Talla

Hukumar dai ta baje wadannan Alkalumman ne ga manema labarai a wurin taron bayyanawa Jam’iyyun kasar shirin da ta yi na gudanar da zabe a tsakkiyar Watan 2 mai kamawa.

Yanzu haka dai ‘Yan Najeriya Miliyan 68 da Dubu 833 da Dari 476 ne suka yanki Katin ta jefa kuri’a, a yayin da Miliyan 42 da Dubu 779 da Dari 339 suka karbi katin ya zuwa yanzu.

Inji Hukumar wannan wata sabuwar dabara ce ta hana Jam’iyyun Siyasa yin magudin zabe a zaben shugaban kasa da na Gwamnoni da Kananan hukumomi da ‘yan Majalisun jihohi da na tarayya da za’a gudanar nan gaba a cikin Watan Fabrairu zuwa Maris na wannan Shekarar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.