Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya yi bayani ne game da tsarin koyar da ilimi ta hanyar amfani da bidiyo wanda daliban Sakandare za su iya kallon darasi a Talabijin ko a kwamfutarsu ko Majigi. Shirin ya tattauna da Malam Nura Muhammad Gaya Malamin da ya samar da fasahar a kwalejin kimiya ta jeka ka dawo ta maza a Kano.
Sauran kashi-kashi
-
Ilimi Hasken Rayuwa Ilimi Hasken Rayuwa, na magana kan halin da karatun yara yan gudun hijira ke ciki a Nijer A wannan makon Shamsiya Haruna ta duba yadda gwamnatin jamhuriyar Nijar ke kokari wajen samarwa yara yan gudun hijira guraban karatu a cikin makarantun bokon kasar gudun kar su yi biyu babu, ba gida ba kasa ba kuma Ilimi.23/05/2023 10:01
-
Ilimi Hasken Rayuwa Karancin dakunan karatu na barazana ga karatun Firamare a Neja Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan kalubalen da karatun Firamare ke fuskanta a jihar Neja ta tsakiyar Najeriya, dai dai lokacin da ake samu karuwar yaran da ke zuwa makaranta.16/05/2023 09:59
-
Ilimi Hasken Rayuwa Ko yaya makomar karatun daliban da aka kwashe daga Sudan take? Shirin na wannan rana, ya duba halin da karatun daliban da suke tsere daga Sudan ke ciki, yayin da rikici ya barke a kasar da ke gabashin Afirka.09/05/2023 10:02
-
Ilimi Hasken Rayuwa Najeriya za ta fara kwashe daliban kasarta da ke Sudan zuwa Masar Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce sun fara tattaunawa da mahukuntan kasar Masar a birnin Alkahira, kan yadda za a kwaso daliban kasar daga Sudan, yayin da bangarori biyu ke ci gaba da gwabza yaki a kasar da ke Gabashin Afirka.25/04/2023 09:58
-
Ilimi Hasken Rayuwa An yaye daliban farko da suka koyi aikin likita a jami'ar Damagaram Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' ya yi tattaki zuwa jihar Damagaram Zendir ta Jamhuriyar Nijar ne, inda jami'ar Damagaram ta yaye daliban farko da suka yi karatun aikin likita. A wannan jami'ar, kuma a wannan rana aka gudanar da bikin karrama malaman sashen koyar da kiwon lafiya da suka samu karin girma, sakamakon nasarar da suka yi ta cin jarabawar kwarewar nan ta hukumar kula da kwarewar malaman jami'o'i a nahiyar Afrika.28/03/2023 09:55