Zaben 2015 a Najeriya

Shugaban Najeriya mai ci Goodluck Jonathan na Jam'iyyar PDP da babban mai adawa da shi tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari na Jam'iyyar APC.
Chanzawa ranar: 16/06/2015 - 11:56

Wannan ne karo na biyar a 2015 da za a gudanar da babban Zabe a Najeriya bayan kawo karshen mulkin Soja a 1999. Shugaba mai ci Goodluck Jonathan na neman wa’adi na biyu inda Jam’iyyarsa ta PDP ke fuskantar babban kalubale daga Dan takarar Jam’iyyar adawa ta APC tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari.