Sarkin Gwandu Mustapha Haruna Jakolo
Wallafawa ranar:
Sauti 04:26
Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC ya lashe zaben Najeriya da rinjayen kuri’u sama da miliyan biyu, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar. Buhari ya doke shugaba mai ci Goodluck Jonathan na PDP wanda shi ne karon farko a tarihin siyasar Najeriya da Jam’iyyar adawa ta doke Jam’iyya mai mulki. Tsohon Dogarin Buhari a zamanin Mulkin Soja Sarkin Gwandu Mustapha Haruna Jakolo ya ce nasarar da Buhari ya samu nasara ce ga 'Yan Najeriya.