Isa ga babban shafi
Najeriya

Zaben Najeriya nasara ce ga Afrika

Na'urar tantance katin zabe ta Card Reader a Najeriya
Na'urar tantance katin zabe ta Card Reader a Najeriya Photo: Reuters/Akintunde Akinleye
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris | Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Majalisar Dinkin Duniya tace nasarar da aka samu a zabukan Najeriya zai bayar da damar gudanar da zabubbuka masu inganci a Yankin Afirka ta Yamma. Jakadan Majalisar a Yankin, Muhammad ibn Chambers ne ya bayyana haka bayan kammala zaben gwamnoni cikin kwanciyar hankali.

Talla

Chambers ya ce hukumar zaben Najeriya ta taka rawar gani, musamman ganin irin matsin lambar da ta samu daga al’ummar kasar da kuma masu sa ido daga kasashen duniya wajen ganin an yi zabe mai inganci.

Chambers wanda ya yabawa shugaban Najeriya mai barin gado Goodluck Jonathan kan rawar da ya taka wajen amincewa da sakamakon zaben, ya ce yana da fata mai kyau cewar za a samu zabubbuka masu inganci a kasahsen Togo da Guinea da Cote d’Ivoire da Burkina Faso a cikin wannan shekarar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.