Najeriya

An shawarci Buhari ya rusa mukaman wasu a Najeriya

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari AFP PHOTO /STRINGER

Kwamitin karbar Mulkin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari karkashin jagoranci Ahmed Joda ya shawarci Shugaban da ya gaggauta sauke mutane da tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ya nada a mukamai daban-daban gab da barin ragamar Mulki.

Talla

Kwamitin ya kuma bukaci Buhari ya sake duba duk wani ayyukan kwangiloli da gwamnatin da ya Shude ya bayar cikin watanin 18 da suka gabata.

A zantawarsa da RFI daya daga cikin Mambobin wannan Kwamitin Barrister Solomon Dalung ya ce kwamitin ya gabatar da wannan bukatar ne domin gani an tabbatar da gwamnati mai Inganci.

Kwamitin dai na gani cewar, akwai mutane da dama da aka dau aiki gab da karewa wa’adin Jonathan a kan mukaman da basu da cancanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.