Najeriya

'Yan damfara na ci gaba da far wa bankunan Najeriya

Shalkwatar babban bankin Najeriya na CBN, dake Abuja
Shalkwatar babban bankin Najeriya na CBN, dake Abuja Wikimedia/Chippla

Wasu alkaluman da aka fitar sun nuna cewa an damfari masu aiyar banki, da ma bankunan Nigeria kudaden da suka haura naira Biliyon 6, cikin shekarar data gabata ta 2014. Rahoton da hukumar dake bayar da inshora ga bakunan kasar wato NDIC ta fitar, ne ya tabbatar da hakan. 

Talla

Rahoton na hukumar ta NDIC, ya nuna cewa akasarin damfarar sun auku ne ta hanyoyin Internet da injinan debi da kanaka na ATM.
Hukumar tace rahotannin damfara daga bankuna sun karu da fiye da kashi 180 cikin 100 a shekarar data gabata, ma’ana damfarar da ake yiwa bankunan kasar da masu hulda dasu ta ninka kenan.
Rahoton yace damfarar da ake yi tayi matukar karuwa daga 3,700 a shekarar 2013, zuwa 10,600 a shekarar data gabata.
Matsalar dafarar da ake wa masu ajiyar banki a Nigeria na kokarin zama ruwan dare, inda sau dayawa ake samun matasa da basu dai aiki sai zaman jiran wanda tsautsayi zai fada wa, su kuma su farwa asusun ajiyar sa.
Yawan dafarar dake gudana a bankunan na Nigeria ke sanya fargaba a zukatan mutane da dama, lamarin da wasu ke dari darin zuba kudadensu a bankunan.
Toh sai dai kuma hukumomin kasar na ci gaba da nemam hanyoyin dakile wannan matsalar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI