Najeriya

Buhari ya bukaci a murkushe Boko Haram nan da watanni uku

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Ofishinsa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Ofishinsa statehouse

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bai wa Manyan hafsoshin tsaron Kasar watanni uku su murkushe Kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da tayar da kayar baya Arewa maso gabashi.

Talla

Shugaban ya kuma bukaci hafsoshin su tabbatar da cewar an kawo karshen garkuwa da mutane da ayyukan ta’adanci da kuma duk wani laifufuka da ake aikatawa a kasar.

Buhari ya bayyana haka lokacin da ya ke rantsar da hafsoshin a ofishinsa, inda ya ke cewar ayyukan wasu batagari sun haifar da rasa rayuka da kuma dukiyoyi, saboda haka ya zama wajibi su hada kan su domin samun nasara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.