Najeriya

An dakatar da shugaban hukumar shige da fice a Najeriya

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari AFP PHOTO /STRINGER

Gwamnatin Najeriya ta bayar da sanarwar dakatar da shugaban hukumar kula da shige da ficen jama’a ta Immigration, yayin da kuma aka ci gaba da binciken jami’an hukumar, bayan da wani dan ta’addan kasar Lebanon yayi runkurin shiga kasar.

Talla

Ahmad al-Assir, da ake nema ruwa a jallo, sakamakon wani mummunan bata kashi da aka yi da sojoji a kasar ta lebanon, ya shiga hannu ne lokacin ya sadada, ya nemi shiga nigerian a ranar Asabar data gabata.
Ya dai yi amfani da Fasfon din bigi ne ta kasar Palasdinu, ya kuma sauya kamanninsa, inda kuma ya sami Visa, wato takardar izinin shiga Najeria.
Wanna yasa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin dakatar da David Shikfu Parradang, cikin gaggawa, don gudanar da binkice.
Dama a zamanin tsohuwr gwamnatin Goodluck Jonathan, hukumar ta kula da shigen jama’a a Najeriya ta shiga halin tsaka mai wuya, bayan da wasu matasa da dama suka mutu, a lokacin da ake je daukar ma’aikatan hukumar, lamarin da ake ganin an tafka almundahana.
Najeriya na fuskantar barazanar tsaro daga ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram, lamarin da ake dangantawa da barin iyakokin kasar ba tare da kwararan matakan tsaro ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.