Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun zabe ta tabbatarwa Jonah Jang kujerar Sanatan Filato ta arewa

Sanata Jonah David Jang, mai wakiltar Filato ta tsakiya
Sanata Jonah David Jang, mai wakiltar Filato ta tsakiya
Zubin rubutu: Nasiruddeen Mohammed
Minti 1

Kotun sauraren kararrakin zabe a Jihar Pilato dake arewacin Najeriya, ta tabbatar da zaben da aka yiwa tsohon gwamna Jonah Jang, a matsayin Sanata mai wakiltar arewacin jihar, a majalisar Dattijan kasar, karkashin jami’iyyar PDP.

Talla

Shugabar Kotun Mai Shari’ah Lanre Akeredolu, tace koken da Ayisa Sambo ta jam’iyyar APC bata da tushe, don haka tayi watsi da kasar, tare da bayar da umarnin APC ta biya diyya ga wadanda ake kara.

Sai dai Jam’iyyar ta APC ta bakin Sakatarenta Bashir Musa Sati, tace da sakel, kuma zasu daukaka kara kan hukuncin, saboda a cewar jam’iyyar, ba a yi mata adalci ba.
Alhaji Bashir yace Alkalin taki basu damar gabatar da shaidu yadda ya kamata, amma kuma a cewar shi, ta baiwa jam’iyyar PDP damar gabatar da nata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.