Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta raba yara miliyan 1.4 da gidajensu

Boko Haram ta kashe mutane da dama a Najeriya da kasashen dake makwabtaka da ita.
Boko Haram ta kashe mutane da dama a Najeriya da kasashen dake makwabtaka da ita. REUTERS/Afolabi Sotunde
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 2

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ta ce Boko Haram ta tilastawa yara miliyan 1.4 barin gidajensu sakamakon jerin hare-haren da ta ke kaddamarwa a Najeriya da kasashen dake makwabtaka da ita na yankin tafkin Chadi.

Talla

A wani sabon rahoto da ta fitar a yau jumm’a hukumar ta UNICEF ta ce hare-haren kungiyar sun tilasta wa kananan yara dubu d 500,000 kauracewa gidajensu a cikin watanni biyar da suka shude a Najeriya kadai, al-amarn da ya jefa rayuwarsu a cikin wahala.

Daraktan Hukumar a yankin yamma da kuma tsakiyar Afrika Manuel Fontaine ya ce alkallumar da hukumar ta tattara daga kashen Kamaru da Chadi da Nijar hade dana Najeriya sun bayyana cewa yara kusan miliyan 1 da rabi ne ayyukan kungiyar Boko Haram suka suka saka cikin wani mawuyacin hali.

Rahotan dake zuwa a dai-dai lokacin da kungiyar ke cigaba da kaddamar da hare-harenta, UNICEF ta tayi hasashen samun karuwan adaddin kananan yara da rikcin ya dai daita daga miliyan 1.5 zuwa 2.1

Hukumar dai ta bukaci karin taimako domin ganin dubban yaran sun ci gaba da zuwa makaranta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.