Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Najeriya ta bada umarnin kama Bukola Saraki

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki REUTERS/Afolabi Sotunde
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 1

Kotun ladabtar da ma’aikata a Najeriya ta bada umarnin kama shugaban Majalisar dattawan kasar, Bukola Saraki.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan kotun ta bude shari’ar zarge zarge 13 da ake yiwa shugaban majalisar Dattawan a yau jumma'a dangane da bada bayanan karya kan kadarorin da ya mallaka.

Lauyan masu gabatar da kara Muslim Hassan ya bukaci kotun ta bada umurnin kama Saraki, abinda kotun ta amince da shi.

Sai dai lauyan dake kare shi Joseph Daudu ya ce zasu daukaka kara a kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.