U17

Super Eaglets sun doke Amurka

Super Eaglets na Najeriya sun doke Amurka ci 2-0 a Chile
Super Eaglets na Najeriya sun doke Amurka ci 2-0 a Chile FIFA/FIFA via Getty Images

‘Yan wasan Super Eaglets na Najeriya da ke rike da kofin gasar duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 sun doke Amurka ci 2-0 a wasannin farko da aka soma a kasar Chile, a ranar Asabar.

Talla

Yanzu Najeriya ce saman teburin rukuninsu na A kuma a gobe Talata ne Super Eaglets za su sake karawa da Chile, Amurka kuma da Croatia.

Chile kuma mai karbar bakuncin gasar ta tashi ne kunnen doki tsakaninta da Croatia.

Guinea kuma ta rike Ingila ne ci 1 da 1.

Brazil ta sha kashe hannun Korea ta Kudu ci 1 da 0.

 A jiya Lahadi Jamus ta bige Australia ne ci 4 da 1.

Mali da Belguim sun tashi ne babu ci.

Argentina kuma ta sha kashe ci 2 da 0 a hannun Mexico.

Ecuador ta lallasa Honduras ci 3 da 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI