Najeriya

Kotun Najeriya ta daure mutane 7 saboda harkar man fetir

Gwamantin Najeriya ta yi alkawarin yakar masu harkar mai a kasar ba bisa ka'ida ba.
Gwamantin Najeriya ta yi alkawarin yakar masu harkar mai a kasar ba bisa ka'ida ba. REUTERS/Jo Yong-Hak/Files

Hukumar da ke ya ki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, wato EFCC ta bayyana cewa Kotu ta yanke wa wasu mutane 7 hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari bayan an kama su da kusan tan dubu 1 da 500 na Man fetur da suka shigo da su cikin kasar ta barauniyar hanya.

Talla

Wannan dai na zuwa ne bayan gwamnatin kasar ta kudiri aniyar sa kafar wando daya da masu harkar man fetur ba bisa ka’ida ba a kasar.

Dukkanin mutanen bakwai ‘yan asalin Najeriya ne, kuma a jiya jumma’a ne babban kotun tarayya da ke jihar Lagos ta same su da aiakata laifin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.