Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da kudirin PDP

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki.
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki. REUTERS/Afolabi Sotunde

Majalisar dattawan Najeriya ta ki amince wa da wani kudurin doka na bai wa matasan kasar marasa aikin yi Naira dubu 5 a kowani wata.

Talla

Sanata Philips Aduda na jam’iyyar PDP ne ya gabatar da kudurin amma bai samu karbuwa ba duk da yunkurin shugaban marasa rinjaye a majalisar, Godswill Akpabio na mara masa baya.

A lokacin da shugaban Majalisar dattawan Bukola Saraki ya gabatar da tambaya danagne da amince wa da kudirin, mambobin jam’iyar PDP mai adawa sun nuna goyon bayan su yayin da mambobin APC mai mulki wadda kuma ke da rinjaye a majalisar suka nuna rashin amincewar su.

Saraki dai ya bukaci Sanatocin da su dau batun rashin aikin yi a Najeriya da muhimmanci ba tare da shigar da siyasa cikin lamarin ba.

A lokacin yakin neman zabe, APC ta yi alkawarin bai wa marasa aikin yi Naira dubu 5 a kowani wata matukar ta lashe zaben, lamarin da ya sa PDP ke matsa mata lamba dangane da cika alkawarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.