Najeriya

A'isha Buhari ta bukaci APC ta cika alkawarinta ga matasa

A'isha Buhar a bayan Shugaba Muhammadu Buhari lokacin rantsar da shi bayan jam'iyarsa ta yi nasara a zaben 2015.
A'isha Buhar a bayan Shugaba Muhammadu Buhari lokacin rantsar da shi bayan jam'iyarsa ta yi nasara a zaben 2015. REUTERS/Afolabi Sotunde

Uwargidan shugaban Najeriya, A'isha Buhari ta bukaci jamiyyar APC mai mulki da ta cika alkawarin da ta dauka lokacin yakin neman zabe na bai wa matasan kasar marasa aikin yi N5,000 a ko wani wata.

Talla

Uwargidan ta bayyana haka a wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakinta kan harkokin yada labarai, Adebisi Ajayi.

Har ila yau, Hajiya A'isha ta bukaci APC ta cika alkawarin bai wa kananan yara a makarantun boko abinci sau daya a kowace rana.

Wannna dai na zuwa ne, mako guda da majalisar dattawan Najeriya ta ki amince wa da wani yunkurin kira ga gwamnatin tarayya domin ciki alkawarin biyan matasa kimanin miliyan 25 da ke zaman kashe wando N5,000 a ko wani wata.

Tuni dai babbar jamiyyar adawa ta PDP ta caccaki APC kan rashin cika wannan alkawarin kuma da ma sanatocin PDP ne suka goyi bayan kudiri kan wannan batun a majalisar dattawan yayinda sanatocin APC da ke da rinjaye suka nuna rashin amincewarsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.