Najeriya

Jam'iyyar PDP ta amsa tafka kura-kurai a Najeriya

Tambarin babbar jama'iyyar  adawa ta PDP
Tambarin babbar jama'iyyar adawa ta PDP

Jam’iyyar PDP ta amsa tafka kura-kurai wajen jagorancin kasar da irin karan-tsayen da ta yi wa al’ummar Najeriya da kuma kuskuren da ta yi wajen tsayar da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar zaben da ya gabata.

Talla

Daya daga cikin jiga-jigan jam’iyar Raymond Dokpesi ya shaida wa manema labarai cewar, suna neman gafara kan kura-kuran da suka yi, musamman na tsayar da tsohon shugaban takara bayan sun yi watsi da shirin karba-karbar da suka shata a tsarin jam’iyyar.

Sakamakon zaben 2015, Jamiyyar PDP ta rasa kujerar shugaban kasa da ta rike tsawon shekaru 16 yayin da kuma APC ta kwace yawancin kujerun PDP a majalisar tarayyar kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.