Najeriya

Shugaba Buhari ya rantsar da ministocinsa

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari statehouse

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da ministocinsa a yau Laraba tare da ayyana ma’aikatun da za su jagoranta.

Talla

Kemi Adeosun  daga jihar Ogun, aka rantsar a matsayin ministar kudi ta kasar, inda kuma tsohon gwamnan Lagos, Baba Tunde Fashola aka rantsar da shi domin kula da ma’aikatar ayyuka da gidaje, yayin da takwaransa na Rivers Rotimi Amaechi ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin ministan sufuri.

Adamu Adamu ne zai jagoranci ma’aikatar ilimi, inda kuma Lai Mohammed zai rike ma’aikatar yada labarai.

An dai gudanar da bikin rantsar da mutane 36 ne a matsayin ministoci a fadar shugaban kasa da ke babban birnin Abuja.

Tuni dai shugaba Buhari ya gargadi ministocin da su dage dantse domin fuskantar kalubalen da ke gabansu.

Ranstuwar dai na zuwa ne bayan majalisar dattawan Najeriya ta tantance dukkanin mutanen da Buhari ya mika mata sunayensu domin tantance su a matsayin wadanda zai nada ministocinsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.