Najeriya

PDP na taron farfado da martabarta

Tambarin babbar jama'iyyar  adawa ta PDP
Tambarin babbar jama'iyyar adawa ta PDP

Yau ne Jam’iyar PDP dake adawa a Najeriya ke gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki a cikinta, wanda ake ganin zai samar mata da sabuwar makoma bayan kayen da ta sha a zaben da ya gabata.

Talla

Kafin dai taron na yau, masu shirya taron ta hannun Raymond Dokpesi sun nemi gafarar al’ummar Najeriya kan abinda suka kira kura-kuran da jam’iyar ta tafka a shekaru 16 da suka gabata, da kin aiwatar da tsarin karba karba, da rashin demokiradiya a cikin gida da kuma tilastawa yan Najeriya shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takara.

Ana sa ran taron zai taka rawar gani wajen dinke barakar da ke tsakanin mambobin babbar jam’iyyar adawar ta PDP.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.