Najeriya

Buhari ya bada umarnin kama Sambo Dasuki

Tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki
Tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki vanguard

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin kama tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki da duk wanda ke da hannun a wajen batar makudan kudaden da aka ware domin sayen makamai amma kuma suka bata ba tare da sayen makaman ba.

Talla

Mai bai wa shugaba Buhari shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya ce, umurnin ya biyo bayan rahotan wucin gadi da Buhari ya karba daga kwamitin binciken sayen makaman da ya kafa wanda ya nuna batar biliyoyin nairori da daloli ba tare da samarwa jami’an tsaron kasar makamai ba.

Rahotan wucin gadin ya nuna cewar hukumomin tsaron kasar da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro sun samu naira biliyan 643 daga shekarar 2007 zuwa watan Maris na shekarar 2015, da kuma wasu dala biliyan 2 da miliyan 193 wadanda ba su hada da kudaden da gwamnatocin jihohi da hukumar DSS da 'yan sanda suka karba ba, amma kadan daga cikin kudaden aka kashe wajen sayen makamai.

Kwamitin binciken ya gano kwangiloli 513 da aka bayar amma kuma daga cikin su kwangiloli 53 na bogi ne wadanda aka biya dala biliyan 2 da miliyan 378 da kuma wasu naira biliyan 13 da miliyan 342 ba tare da gudanar da aikin ba.

Rahotan ya ce kudaden da gwamnati ta biya wajen irin wadannan kwangilolin da ba’ayi ba sun zarce bashin dala miliyan guda da gwamnati ta karba dan sayo makamai.

Kwamitin ya kuma gano wasu naira biliyan 3 da miliyan 850 da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya biya wani kanfani guda ba tare da wata takardar kwangila ba.

Rahotan ya ce tsakanin watan Maris na shekarar 2012 zuwa Maris na shekarar 2015, Kanar Sambo Dasuki ya bada kwangilolin bogi da kudin su ya kai naira biliyan 2 da miliyan 219, da wasu dala biliyan 1 da miliyan 671 da kuma euro miliyan 9 domin sayen jiragen yaki 4, helikopta 12, bama bamai da alburusai wadanda ba’ayi kwangilar ba kuma ba a mika wa rundunar sojin sama makaman ba.

Sanarwar ta ce tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanar Dasuki ya umurci babban bankin Najeriya ya sanya dala miliyan 132 da euro miliyan 9 a asusun wani kamfani da ake kira Societe D’equipmente Internationaux a Afika ta Yamma, Birtaniya da Amurka ba tare da sanin ko na menene ba, kuma babu takardar kwangila.

Binciken ya nuna damuwa sosai kan yadda aka yi ta karkatar da kudaden yayin da sojojin Najeriya da ke yaki da kungiyar Boko Haram ke fama da karancin makamai da kayan aiki.

Adeshina ya ce shugaba Muhammadu Buhari, ya bukaci kama daukacin masu hannu cikin badakalar dan hukunta su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI