Najeriya

Harin bam ya hallaka mutane 15 a kano

Jihar Kano ta fuskanci hare haren bama-bamai a baya
Jihar Kano ta fuskanci hare haren bama-bamai a baya REUTERS/Stringer

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano da ke Najeriya, Muhammad Musa Katsina ya tabbatar da mutuwar mutane 15 a harin tagwayen bama-bamai da aka kai kasuwar wayoyin hannu ta unguwar Farm center da ke birnin.

Talla

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa kimanin mutane 53 sun jikkata a harin wanda aka ce wasu 'yan mata biyu ne suka kaddamar da shi a yammacin jiya .

Wasu da al'amarin ya faru akan idanunsu, sun bayyana cewa, bam na farko ya tashi ne a kofar shiga cikin kasuwar yayin da na biyu ya tashi a tsakiyar kasuwar.

Wakilin RFI hausa daga Kano, Abubakar Isa Dandago ya ce, ya kidaya gawarwakin mutane 11 da hannunsa cikin su har da ta daya daga cikin 'yan matan da suka kai harin.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu da kaddamar da wani kazamin harin bam a birnin Yola na jihar Adamawa, inda mutane sama da 30 suka rasa rayukansu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI