Najeriya

An shirya gudanar da zaben jihar Bayelsa

Tambarin hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta wato INEC.
Tambarin hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta wato INEC.

A gobe asabar ne al-ummar jihar Bayelsa da ke yankin Niger Delta a Najeriya za su gudanar da zaben gwamna.

Talla

Gwamnan jihar mai ci Seriake Dickson mai shekaru 49 da haihuwa shi ne zai wakilci jam’iyyar PDP a fafatawa tsakaninsa da Timpire Sylva mai shekaru 51 da haihuwa wanda kuma ke neman kujerar karo na biyu a karkashin jam’iyyar APC .

Matukar Sylva ya lashe zaben dai, to lallai hakan na a matsayin babbar nasara ga jam’iyyar APC wadda ke mulki Kasar.

Bayelsa dai ita ce jihar tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan na PDP kuma a lokacin zaben shugaban kasa na 2015, PDP ta samu kashi 98 cikin 100.

Tuni dai aka tura jami’an ‘yan sanda 14,000 saboda dari-darin da ake yi dangane da yiwuwar barkewar tarzoma a zaben.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.