Najeriya

Zaben Rivers: Kotu ta goyi bayan sake zaben gwamna

Kotu na bukatar sake gudanar da zaben Rivers nanda kwanaki 90
Kotu na bukatar sake gudanar da zaben Rivers nanda kwanaki 90 AFP/Pius Utomi Ekpei

Kotun daukaka kara da ke babban birnin Abuja na Najeriya ta goyi bayan hukuncin da kotun sauraren korafe korafen zabe ta jihar Rivers ta yanke na soke zaben gwamnan jihar, Nyesom Wike, inda ta bayar da umarnin gudanar da sabon zabe nan da kwanaki 90.

Talla

Kotun ta bayyana cewa ta gamsu da hukuncin karamar kotun na soke zaben wanda aka yi a ranar 11 ga watan Aprilun wannan shekarar, in aka bayyana Wike na jam’iyyar adawa ta PDP a matsayin wanda ya lashe.

To sai dai an yi zargin cewa an yi magudi a zaben bayan na’urar kada kuri’u,CARD READER ta samu matsala.

Hukuncin dai na zuwa ne bayan Dakuku Peterside na jam’iyyar APC da kuma ya kalubalanci Wike a zaben na gwamna, ya shigar da kara kotun.

A bangare guda, Wike ya lashi takobin kalubalantar hukuncin a kotun koli ta kasar kuma ya jaddada wa al-ummar jihar Rivers cewa, zai ci gaba da zama a kujerar gwamna har zuwa lokacin da kotun kolin za ta yanke nata hukuncin.

Tun a shekara ta 1999 ne jam’iyyar PDP ke shugabanci a jihar Rivers.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.