Najeriya

Buhari zai ci gaba da yaki da cin hanci a Najeriya

shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a lokacin tattaunawarsa da Manema labarai a Abuja.
shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a lokacin tattaunawarsa da Manema labarai a Abuja. tadall.com

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa don tabbatar da cewar an kwato makudan kudin da jami’an gwamnati suka sace. 

Talla

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a jiya laraba, shugaban ya ce suna da shaidun da ke nuna musu yadda aka yi rub da ciki da kudaden jama’a kuma za su mika wa hukumomin shari’a don hukunta ma su hannu a ciki.

Dangane da rikicin da aka samu tsakanin shugaban sojin Najeriya da mabiya Shia a Zaria, Buhari ya ce ba zai ce komai ba sai hukumomin da ke bincike sun kammala ayyukansu.

Dangane da yaki da Boko Haram kuwa, shugaban ya ce sojojin Najeriya sun yi nasarar hana kama garuruwa ko kananan hukumomi da kungiyar ke yi, inda suka koma kai harin kunar bakin wake.

Dangane da 'yan matan Chibok kuwa, shugaban ya ce muddin aka samu sahihancin shugabanci a kungiyar Boko haram, kuma su ka yi alkawarin mika 'yan matan za su tattauna da kungiyar don ganin an sako 'yan matan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.