Najeriya

Kotun Kano ta yanke wa Abdul Inyas hukuncin kisa

Mabiya addinin musulunci na girmama Annabi Muhammadu.
Mabiya addinin musulunci na girmama Annabi Muhammadu. REUTERS/Staff/Files

Wata babbar kotun addinin musulunci a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan Abdul-Aziz Dauda da aka fi sani da Abdul inyas, bayan ta same shi da laifin furta kalaman batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi.

Talla

Rahotanni sun ce a baya, Abdul Inyas ya gudu kafin daga bisani a cafke shi kana aka gurfanar da shi a  gaban babbar kotun shari'ar.

A watan mayun bara ne, Abdul Inyas ya furta kalaman a wajen wani taron maulidin Sheik Ibrahim Inyas, abinda ya fusata jama'a yayin da malaman addinin musulunci suka yi tir da abinda ya aikata.

An dai yanke masa hukunci ne a sirce amma ana ganin yana da damar daukaka kara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.