Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaba Buhari na ziyarar kwanaki uku a UAE

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP PHOTO / SAJJAD HUSSAIN
Minti 2

A yau Lahadi ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke fara ziyarar kwanaki uku a haddadiyar daular larabawa wato Dubai.

Talla

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ya fitar, Garba Shehu ta bayyana cewa, Buhari zai hadu da sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Ban ki-Moon da yarima Mohammed bin Zayed na Abu Dhabi a taron makamashin samar da wutar lantarki na duniya na wannan shekarar.

Har ila yau shugaba Buhari zai jagoranci tawagar ministocinsa a tatttaunawar da za su yi da gwamnatin hadaddiyar daular larabawa, inda ake sa ran za su cimma yarjejeniya kan
batutuwan da suka shafi tattalin arziki da huldar kasuwanci.

A bangare guda, ana sa ran daular larabawan za ta taimaka wa Najeriya dangane da kokarinta na yaki da ta’addanci da kuma yaki da cin hanci da rashawa musamman a wannan loacin da ta dukufa wajen kwato kudaden gwamnati da aka sace a baya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.