Isa ga babban shafi
Najeriya

Kashi 45 cikin 100 na masu ilimin jami'a basu da aikin yi a Najeriya

Abuja,babban birnin Najeriya
Abuja,babban birnin Najeriya Wikimedia Commons/Bryn Pinzgauer
Zubin rubutu: Ramatu Garba Baba
Minti 2

Sabon bincike ya tabbatar da cewa kashi 45 cikin 100 na masu ilimin jami’a a Najeriya basu da aikin yi, wani kanfani dake samarwa jama’a aiki a kasar ya bukaci samar da mafita don magance wannan matsala mai matukar illa ga ci gaban kasar

Talla

Sakamakon binciken na yau litinin ya nemi hadin kan gwamnati dama kanfanoni masu zaman kansu da su dauki matakin warware wannan matsala ta hanyar samar da aikin yi ga matasan kasar, ganin rawar da  zaman kashe wando a tsakanin matasa ta taka a yaduwar ayyukan  kungiyar Boko Haram  a kasar.

Binciken ya bukaci baiwa matasa horo a sana’oi musanman wadanda suka kammala karatunsu na Degree don dogaro da kansu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya zayyana talauci da rashin adalci da kuma rashin aikin yi a matsayin musabbabin tashe tashen hankula da aka samu a wasu sassan kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.