Najeriya

Mutane 14 suka mutu a harin Chibok

Yankin Chibok inda Mayakan Boko Haram suka ce 'Yan Mata sama da 200.
Yankin Chibok inda Mayakan Boko Haram suka ce 'Yan Mata sama da 200. news.softpedia
Minti 2

Akalla mutane 14 suka mutu a wasu hare haren kunar bakin wake guda uku da ‘Yan Boko Haram suka kai a garin Chibok na jihar Borno a Najeriya inda suka sace Mata ‘yan Makaranta sama da 200.

Talla

Ana hasashen cewa adadin mamatan na iya karuwa, lura da yawan mutane fiye da 30 da suka samu munanan rauni.

A garin na Chibok ne dai mayakan Boko Haram su ka yi awon gaba da mata sama da 200 a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 kuma har yanzu babu labarinsu.

Rahotanni sun ce, wasu 'yan mata uku ne suka kaddamar da harin na kunar bakin wake a yayin da ake cin kasuwar garin.

Wani mazauni garin ya shaidawa RFI Hausa cewa da misalin karfe 11 na rana ne aka kai harin.

Wani namiji ne ya kai hari na farko akan hanya, sannan mata ne suka tayar da bama bamai a bakin kasuwa a cewar mazaunin garin na Chibok.

Babu dai wani bayani daga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari game da harin wanda yanzu haka ke ziyara a Kenya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.