Najeriya

Zanga-zangar adawa da karin kudin Wutan lantarki a Najeriya

Gangamin 'ya'yan Kungiyar Kwadago a Jihar Osun kwananki baya
Gangamin 'ya'yan Kungiyar Kwadago a Jihar Osun kwananki baya

A ranar Litinni mai zuwa Rassan Kungiyar kwadago a Najeriya zai kaddamar da zanga-zangar adawa da Karin kudin wutar lantarki a kasar.

Talla

Shugaban Kungiyar ta Kasa Ayuba Wabba ya ce zanga-zangar za ta karade birnin Tarayyar Abuja da kuma sauran rassanta da ke Jihohin kasar 36.

Shugaban ya kuma bukaci wadanda Karin wutan bai gamsar dasu ba, su fito kwansu da kwarkwarta domin nuna adawarsu.

A cewar Ayuba daukan wannan mataki ya zama wajibi, dan Gwamnati ta yi waiwaye kan Karin da ta yi na kashi 45 cikin 100 da ya sabawa dokoki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.