Najeriya

PDP ta nada Modu Sheriff a matsayin shugabanta

Sabon shugaban jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Ali Modu Sheriff.
Sabon shugaban jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Ali Modu Sheriff. dailypost.ng

Babbar jam’iyyar adawa a tarayyar Najeriya PDP ta tabbatar da tsohon gwamnan jihar Borno Ali Modu Sheriff a matsayin sabon shugabanta na kasa.

Talla

Jam’iyyar PDP wadda ta mulki Najeriya tsawon shekara 16, ta kasance ba ta da shugaba tun bayan da Adamu Mu’azu ya sauka daga mukaminsa cikin shekarar bara bayan an kammala zaben 2015.

To sai dai Uche Secondus  ya tafiyar da jam'iyyar na wani dan lokaci a matsayin shugaba mai rikon kwarya yayin da a yanzu Modu Sheriff ya karme ragama daga hannunsa

Tuni dai aka rantsar da Modu Sheriff domin kama aiki kamar yadda mai magana da yawun jam’iyyar Olisa Metuh ya shaida wa maneman labarai.

A zantawarsa da manema labarai, sabon shugaban ya yi alkawarin gudanar da aiki tukuru domin sake gina jam’iyyar ta PDP har ta sake kafa gwamnati a shekara ta 2019.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.