Najeriya

PDP za ta karbi mulkin Najeriya a 2019- Sheriff

Sabon shugaban jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Ali Modu Sheriff.
Sabon shugaban jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Ali Modu Sheriff.

Sabon shugaban jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Ali Modu sheriff, ya lashi takobin jagorantar jam’iyyar har ta kai ga sake samun nasarar shugabantar kasar a shekara ta 2019.

Talla

Sheriff wanda ke magana a taron murnar tabbatar da Mr.Okezie Ikpeazu a matsayin gwamnan jihar Abia, ya bayyana cewa, babu abinda zai dakatar da jam’iyyarsa daga karbe ragamar mulkin jam'iyyar APC nan gaba duk da dai ta sha kashi a zaben 2015 da aka gudanar.

Sabon shugaban dai na cikin mambobin da suka kafa jam’iyyar APC amma ya sauya sheka zuwa PDP a shekara ta 2014.

Kawo yanzu dai shugaba Muhammadu Buhari bai bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a 2019 ba da zaran wa’adinsa ya kare.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.