Najeriya

EFCC ta cafke tsohon shugaban PDP a Najeriya

Tsohon mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP ta Najeriya, Uche Secondus
Tsohon mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP ta Najeriya, Uche Secondus sholido.com

Rahotanni daga Najeriya na cewa hukumar yaki da rashawa a kasar EFCC ta cafke tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus bisa zargin karbar wadannsu motocin Bus wadanda kuma hukumar ta EFCC ke neman ya dawo da su.

Talla

Ana zargin Secondus ya karbi motoci 23 da kudinsu ya kai Naira miliyan 310 ba bisa ka’ida ba daga hannun wani dan kusawa Jide Omokere wanda ke fitar da man fetir akai akai ba tare da biyan gwamnati ba.

Daraktan yada labarai na jam’iyyar ta PDP Adeyanju Ayodeji, ya tabbatar da kama Secondus, yayin da kuma wata sanarwar jam’iyyar ke zargin jam’iyyar APC da hannu wajen kama shi, tare da fadin cewa suna da masaniya a game da wani yunkurin kama mataimakin shugaban majalisar dattawa wanda dan jami’iyyar ne wato Sanata Ike Ekweremadu, da shugaban marasa rinjaye a majalisar Sanata Godswill Akpabio da dai sauransu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.