Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta ci gaba da fama da karancin mai

Karamin ministan mai na Najeriya Mr. Ibe Kachikwu.
Karamin ministan mai na Najeriya Mr. Ibe Kachikwu. AFP PHOTO / STRINGER

Ministan kasa a ma’aikatar mai ta tarayyar Najeriya Ibe Kachikwu, ya ce za a ci gaba da fuskantar matsalar mai a kasar har nan da watanni biyu masu zuwa.

Talla

Mr.Kachukwu ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da aka yi a jiya tsakanin shugaban kasar Muhammadu Buhari da kungiyoyin ma’aikatan mai na kasar.

Ministan ya ce, an fuskanci matsaloli ta fannin samar da mai a cikin gida, lamarin da ya sa ana shigo da man kashi 100 bisa 100 daga waje a maimakon kashi 50 cikin dari.

A duk lokacin da aka samu karancin mai dai, al'ummar Najeriya na kokawa saboda matsanancin halin da suke samun kan su a ciki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.