Najeriya

Mutane miliyan 2 sun rasa gidajensu a Najeriya

Boko Haram ta raba mutane da dama da muhallansu
Boko Haram ta raba mutane da dama da muhallansu REUTERS/Albert Gonzalez Farran

A Najeriya, kusan mutane miliyan biyu ne da suka kaurace wa gidajensu saboda rikicin Boko Haram, ke zaune a sansanoni daban daban na ‘yan gudun hijira da ke jihohin Borno da Yobe da Taraba da Gombe da Bauchi har ma da Adamawa.

Talla

Babban jami’in hukumar bayar da agajin gaggauwa ta Najeriya, Sa’ad Bello ya sanar da haka a lokacin da jakadiyar Amurka a majalisar dinkin duniya Samantha Power ta ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira na Malkohi da ke jihar Yola.

Mr. Bello ya ce, gwamnatin Najeriya na kokarin samar da bukatun mazauna sansanonin, kama daga abinci da magunguna har ma da tsaro.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.