Brittaniya-Najeriya

Cin hanci ya yiwa Najeriya katutu inji Cameron

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Firaministan Birtaniya a London
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Firaministan Birtaniya a London REUTERS/Neil Hall

Yayin da ake shirin fara taron shugabannin kasashen duniya kan yaki da cin hanci da rashawa, Firayi ministan Birtaniya David Cameron ya bayyana Najeriya da Afghanistan a matsayin kasashen da akafi cin hanci a duniya.

Talla

Kafofin yada labarai sun jiyo Cameron na shaidawa Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta 2 cewar ya gayyato shugabannin kasashen da cin hanci ya yiwa katutu Najeriya da Afghanistan, inda nan take Arch Bishop na Kanatabori Justin Welby ya wanke shugaba Buhari daga cin hancin.

Tuni dai wannan batu ya harzuka yan Najeriya da dama inda suke cewa ya dace shugaban kasar Muhammadu Buhari da yanzu haka ke kasar Brittaniya don hallatar taron da zai mayar da hankali kan batun cin hanci da rashawa da ya kauracewa taron ya kuma dawo gida Najeriya .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.