Najeriya

Majalisar na tattaunawa kan farashin mai a Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya za ta gana da ministan mai na kasar kan karin farashin man fetir.
Majalisar wakilan Najeriya za ta gana da ministan mai na kasar kan karin farashin man fetir. AFP

Majalisar wakilan Najeriya za ta yi zama na masamman a wanann Litinin tare da karamin ministan man fetur na kasar, Ibe Kachikwu domin tattaunawa kan karin farashin mai daga Naira 86 zuwa 145 akan lita guda.

Talla

A makon jiya ne Mr. Kachikwu ya sanar da matakin gwamnatin kasar na kara farashin man, abinda ya haifar da cece-kuce a dukkanin fadin kasar.

Mataimakin shugaban kasar, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, ya zama dole a dauki matakin saboda halin tawaya da asusun waje na kasar ya shiga.

Tuni dai kungiyar kwadago ta kasar ta bai wa gwamnatin wa’adi zuwa gobe Talata da daddare da ta janye matakinta na cire tallafin man fetir din, ko kuma ta shiga yajin aiki na gama gari.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.