Najeriya

NLC ta janye yajin aiki a Najeriya

Wasu daga cikin mambobin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC.
Wasu daga cikin mambobin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC.

Kungiyar kwadago ta Najeriya karkashin shugabanta Ayuba Waba, ta janye yajin aikin game gari da ta fara a ranar labarar da ta gabata.

Talla

Kungiyar ta shiga yajin aikin ne domin nuna adawarta da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na kara farashin man fetir zuwa naira 145 daga Naira 86 a kan kowacce lita guda.

Wannan al’amari dai ya haifar da cecekuce a dukkanin fadin kasar, inda wasu ke marhaba da matakin janye tallafin man fetir yayin da wasu kuwa ke nuna akasin haka.

Gabanin janye yajin aikin a wannan Lahadin, sai dai kungiyar ta yi ta zanta wa da wakilan gwamnati domin cimma matsaya akan batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI