Najeriya

Buhari ya fasa ziyarar Legas a yau

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari AFP PHOTO / SAJJAD HUSSAIN

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dage ziyarar kwanaki biyu da ya shirya kawowa jihar Legas a wannan Litinin.

Talla

Mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu ya ce, an dage ziyarar har nan da bayan azumin watan Ramadan da ake sa ran farawa a cikin wata mai zuwa.

A halin yanzu Buhari na kan fuskantar ayyuka daban daban da lokutansu ke karo da juna, abinda Garba Shehu ya bayyana a matsayin abu mai wahala ga shugaban.

An dai shirya ziyarar ce domin Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka da aka kammala a jihar ta Legas amma dai mataimakinsa, Yemi Osinbajo zai wakilce shi a wani yanayi da ba zai dauki hankulan jama’a ba.

Osinbajo zai kaddamar da kananan ayyukan na Legas amma sauran zai bar wa Buhari har zuwa bayan azumin Ramadan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI