Najeriya

Tsagerun Niger Delta sun tarwatsa bututun Agip

Sabuwar kungiyar tsagerun Niger Delta ta kaddamar da wani sabon hari kan bututun man fetir mallakin kamfanin Agip ENI da ke jihar Bayelsa a tarayyar Najeriya.

Kungiyar Niger Delta Avengers na ci gaba da tayar da kayar a Najeriya
Kungiyar Niger Delta Avengers na ci gaba da tayar da kayar a Najeriya AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Kungiyar mai suna Niger Delta Avengers, ta sanar da haka a safiyar yau jumma’a a shafinta na Twitter, inda ta ce bututun da ta tarwatsa shi ne mafi girma da kamfanin ke amfani da shi a jihar.

Kungiyar ta nuna farin cikinta kan yadda matatun mai na kasashen waje suka katse siyan mai daga Najeriya kamar yadda ta ce, yayin da ta zargi Najeriyar da sace albarkatun mai da iskar gas da Allah ya hore wa yankin na Niger Delta.

Har ila yau tsagerun sun ce, za su sanar da kasashen duniya lokacin da za su fara huldar kasuwanci da su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI